Dole mu gyara kasar mu da kan mu - Inji Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari a jiya Juma'a ya bayyana cewa dole ne 'yan Najeriya su warware matsalolin su da kansu a tsakanin su don kuwa ko wace kasa matsalolin ta daban ne.

Shugaban yayi wannan jawabin ne a yayin da yake karbar bakuncin manyan jami'an dake halartar makarantar koyon ayyuka da tsari don cigaba watau National Institute for Policy and Strategic Studies a turance dake a garin Kuru a fadar sa dake a Abuja.

Dole mu gyara kasar mu da kan mu - Inji Shugaba Muhammadu Buhari

Hausansi dai ta samu cewa shugaba Buhari din ya kuma nuna jin dadin sa game da yadda 'yan kasar suka dage wajen yin noma tukuru don magance matsalar abinci a cikin kasa.

Daga karshe kuma sai ya bayar da tabbacin cewa lallai gwamnatin sa zata ci gaba da bayar da gudummuwar ta da cikakken goyon baya domin ganin samun tabbataccen ci gaba mai dorewa.

Labels: