Dokar hana kiwo: Wasu makiyaya na ci gaba da sha'aninsu a jihar Benue


Dokar hana kiwo da aka sanya a jihar Benue ya fara aiki
- Wasu daga cikin makiyaya a jihar sunyi burus da dokar
Rahotanni sun kawo cewa duk da dokar hana kiwo da gwamnatin jihar Benue ta kafa, har yanzu wasu makiyaya basu fara aiki da dokar ba.
Sashin BBC Hausa ta ruwaito cewa ta kai ziyara garin Makurdi, babban birnin jihar ta Benue, sannan kuma ta tarar da makiyaya suna ci gaba da sha’aninsu na kiwon dabbobi.
Gwamnatin jihar Benue dai ta sanya dokar hana kiwon dabbobi wacce ta fara aiki tun a ranar 1 ga wannan wata na Nuwamba da muke ciki.
Sannan kuma gwamnatin ta sha alwashin hukunta duk mutumin da yak eta mata dokarta sannan kuma zata ci shi tara ko kuma ta mika shi gidan wakafi na tsawon wasu lokaci.

Labels: