Diezanigate: EFCC ta kama tsohon gwamnan Benuwe, Suswam

EFCC na zargin Gabriel Suswam da soke kudaden da Diezani ta turo masa don a nemawa Goodluck komawa kujerar shugaban kasa a 2015.
A yau Alhamis hukumar yaki da cin-hanci da rashawa, EFCC, tayi dirar mikiya a kan tsohon gwamnan jihar Benuwe, Gabriel Suswam, da tambayoyi a bisa zargin har da shi aka ci kudin zaben da Diezani da raba a zaben 2015 har Naira biliyan 23.
Bayan wannan, ana zargin Suswam da yin kwana da kudin al'ummar jihar sa har sau karo goma.
EFCC ta tambaye shi a kan kason kudin zaben da aka turo masa har Naira milyan 450 ta asusun bankin sa, a kan me yayi da su.
Har yanzu dai maganar bata gama fitowa ba a kan ya yayi da su.

Labels: