- An zargi Kurfi da nuna wa yan Izala fifiko sama da yan Darikar dake mazabar sa
- Danlami Kurfi ya karyata zargin da ake masa
Dan majalisar wakillai dake wakiltar mazabar Dutsinma/Kurfi, Danlami Mohammed Kurfi ya tsallake rijiya da baya yayin da matasa suka kai masa hari a mazabar sa.
Al’ummar mazabar sa, sun kai masa hari ne saboda rashin cika alkawran da ya dauka.
Dan majalisar ya tabbatar wa jaridar Vanguard aukuwar wannan lamari.
Kurfi yace matasan sun kai mu shi hari ne saboda ayyukan gwamnati da ya raba a mazabar sa.
Danlami Kurfi ya tsallake rijiya da baya yayin da mutanen mazabar sa suka kai ma sa hari saboda rashin cika alkawaran da yayi mu su
An zargi Kurfi da nuna ma wata aqidar addini fifiko akan wata aqida wajen raba ayyukan.
Kurfi ya ce harin da aka kai masa aikin makiyan sa ne wanda ba sa son cigaban sa da na al’umma.
Kurfi ya karyata zargin da ake masa na cewa yafi ba yan kungiyar Izala fifko sama da yan Darikar dake mazabar sa.
“Dan majalissar ya ce kwanakin baya ya saya wa yan kungiyar Darika makarantar Islamiya da ya kai kimanin naira miliyan daya, saboda haka ba gaskiya bane ace baya son yan darika.
Kurfi ya ce an raba ayyukan ne bisa cancanta, ba son zuciya ba.
Labels: Labarai