Da wanne za a aji: Ana shirin kama Mahaifiyar Maryam Sanda

Hukumar ICPC za ta kama Mahaifyar Maryam Sanda

- Ana zargin ta da satar wasu kudi da kuma yin sharri

- Yanzu haka za a maka ta a Kotun da ake karar diyar ta

Mun samu labari cewa an fara shirin damke Hajiya Maimuna Aliyu wanda ita ce Mahaifiyar Maryam Sanda da ake zargi ta kashe Mijin ta a makon da ya wuce har lahira.

Hajiya Maimuna Mahaifiyar Maryam Sanda

Hukumar ICPC za ta kama Mahaifyar Maryam Sanda kamar yadda labari ya zo mana daga Jaridar Daily Trust ta kasar. Ana zargin Hajiya Maimuna da yin gaba da wasu makudan kudi na Kamfanin Aso Savings da kuma yi wa wani Jami’in Hukumar sharri.

Ana zargin Maimuna da saida wasu manyan filaye har 3 a Unguwar Jabi da ke Abuja da sunan Kamfanin Aso Savings amma ta yi gaba da kudin har Naira Miliyan 57. Bayan nan kuma ta sabawa dokar Hukumar ICPC inda tayi wa wani babban Jami’i kage.

Hukumar ICPC da ke yaki da cin hanci da rashawa a kasar tace za ta maka Maimuna Aliyu a Kotun da yanzu haka ake karar diyar ta Maryam Sanda wanda ake zargi da kashe Mijin ta. Kwanaki Shugaba Buhari ya ba Maimuna mukami amma dole aka karbe.

Labels: