Cif John Oyegun ya bayyana shirin shugaba Buhari ga 'yan Najeriya

Shugaban APC, Cif John Oyegun ya bayyana shirin shugaba Buhari ga 'yan Najeriya

- Oyegun ya ce shugaba Buhari na iya kokarinsa don inganta rayuwar al’ummar Najeriya

- Oyegun ya bayyana cewa APC na da kudurin sake mayar da Najeriya a kan hanyar ci gaba

Cif John Oyegun, shugaban jam'iyya mai mulki ta APC, ya ce shugaban kasa, Muhammadu Buhari na iya kokarinsa don inganta rayuwar al’ummar kasar, ya bukaci dukkan 'yan Najeriya su ba da goyon bayan da ake bukata ga gwamnatin.

Oyegun ya yi wannan bayani a Uyo ranar Asabar, 18 ga watan Nuwamba, yayin da yake kaddamar da yakin neman zabe na APC a Akwa Ibom, wanda za a yi ranar 2 ga watan Disamba.

Oyegun ya ce: "Shugabanku na iya kokarinsa don ganin cewa abubuwa sun daidai ta nan ba da jumawa ba. APC na bukatar mutane masu hangen nesa, mutane masu sha'awar kawo ci gaba ga sabuwar Najeriya".

Cif John Oyegun, shugaban jam'iyya mai mulki ta APC

Kamar yadda Hausansi ke da labari, Oyegun ya bayyana cewa APC na da kudurin sake mayar da Najeriya a kan hanyar ci gaba ta hanyar kawar da cin hanci da rashawa da almubazzaranci da dukiyoyin al’umma.

Ya ce ya yi matukar murna game da yawan taron jama'a, inda ya bayyana hakan a matsayin alamar cewa mutanen Akwa Ibom suna shirye su rungumi canji na gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Oyegun, wanda ya karbi wasu ‘ya’yan jam’iyyar adawa ta PDP da suka yi sheka zuwa APC a karkashin jagorancin sanata Nelson Effiong, wanda ke wakiltar Akwa Ibom ta Kudu a jihar, ya ce APC na alfahari da jihar.

Labels: