Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2018 a yau

Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2018 a yau

- A ranar 2 ga watan Nuwamba ne shugaban kasar ya aika wasika ga majalisar dattawa da wakilai

- Ana sa ran za’a gabatar da kasafin kudin ne da misalign karfe 2:00 na rana

Rahotanni sun kawo cewa a yau Talata, 7 ga watan Nuwamba shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2018, a gaban majalisar dokokin Najeriya.

Wannan shine karo na uku da gwamnatin Buhari zata gabatar cikin kasafin kudi da ya ta’allaka akan nema domin babu adanannun kudi.

A ranar 2 ga watan Nuwamba ne shugaban kasar ya aika wasika domin sanar da majalisar dattawa da majalisar wakilai batun gabatar da dokar dacewa.

Hasashe sun nuna cewa kasafin kudin wannan karo ka iya shan bam-banm da na sauran shekarun da suka gabata, saboda a yanzu gangar man fetur ta haura zuwa kusan dala sittin.

A watannin da suka gabata, shugaba Muhammadu Buhari, ya yi ta kokawa musamman akan yadda tsagerun Niger-Delta ke fasa bututun mai, koda yake, wannan matsalar ta kare duk da barazanar da ‘yan tsagerun suka yi ta dawo da kai hare-hare.

Ana sa ran za’a gabatar da kasafin kudin ne da misalign karfe 2:00 na rana.

Labels: