Buhari ya sha ruwan sarautu a wurin sarakunan kabilar Igbo

Ziyarar da shugaba Buhari ya kai yankin kudu maso gabas ta samu tagomashi domin kuwa sun karrama shi da manyan sarautu.

A ranar litinin kungiyar sarakunan kabilar Igbo ta yi wa Buhari nadin sarautar "shugaban shugabannin kabilar Igbo (Ochi Oha Ndigbo) da kuma sarautar "Abokin Amana (Enyi Oma)" a jihar Ebonyi.

Buhari ya sha ruwan sarautu a wurin sarakunan kabilar Igbo

Sannan gwamnan jihar Ebonyi ya karrama shugaba Buhari da kyautar buhun shinkafa 2,000 'yan Ebonyi da kuma Doya guda 2,000.

Shugaba Buhari ya sadu da shugaban kungiyar kabilar Igbo ta "Ohaneze Ndigbo", Cif John Nnia Nwodo wanda ya kasance tsohon gwamnan jihar ta Ebonyi, da kuma manyan shugabannin kungiyoyin addini dana gwamnatin jihar Ebonyi.

Ana sa ran shugaba Buhari zai kasance a filin wasa na PA Ngele Oruta dake Abakaliki domin tattaunawa da jama'ar yankin a bangarorin rayuwa daban-daban.

Labels: