- Mu'azu Magaji, jigo a APC, ya yi kira ga Buhari da ya ja gefe ya rabu fitowa takara a 2019
- Magaji ya fadi wannan maganan lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja
- Magaji yace shugaba Buhari yana iya kokarin sa amma matsalolin Najeriya sun yi masa yawa
Mu'azu Magaji, wanda jigo ne a APC na Jihar Kano ya shawarci Buhari da ya yi biris da wadanda su ke karfafa masa gwiwar yin tazarce a 2019. Magaji ya yi nuni da cewan ko shi Buhari ya yi korafin yawan shekarun sa sa'adda ya karbi mulki a 2015.
Buhari ya manta da burin sa na 2019 - Magaji, jigo a APC
Magaji ya bayyana hakan ne ga manema labarai a Abuja. Ganin yadda siyasar yanzun ta ke da kuma kalubalen da ke akwai, Magaji ya ce ya kamata Buhari ya rufa ma kan shi asiri ya ja gefe, salin-alin don ba wa matashin dan siyasa dama.
A cewar Magaji, Buhari ya yi iya nasa kokarin ga Kasar nan. Sai dai kuma gaza magance matsalolin Kasar nan a gareshi na iya bata masa suna. Ga dukkan alamu kuma, magance su gareshi na da matukar wuya.
Ya kara da cewa, abun da ya kamata shi ne Buhari ya nemo mutane masu amana da adalci da gaskiya don su ja ragamar Kasar, su ci gaba daga inda ya tsaya.