Boss Mustapha: Abin da sabonSGF ya ce game da Lawal daBuhari

Sabon seketaren gwamnatin Najeriya ya ce
shugaba Buhari mutum ne mai matukar
tausayin yan Najeriya
- Mustapha ya ce hakkin su ne su tabbatar
da gwamnatin APC ta samu nasara a
Najeriya
- Boss Mustapha ya yaba da kokarin Lawal a
ofishin Sektaren gwamnatin tarayya
Sabon seketaren gwamnatin tarayya da
aka rantsar a jiya Laraba 1 ga watan
Nawumba, Boss Mustapha ya ce
shugaban kasa Muhammadu Buhari
mutum ne mai matukar tausayi yan
Najeriya.
Boss ya tabbatar da cewa gwamnatin
jam’iyyar APC za ta dawo da martaba da
kimar Najeriya a cikin kasashen duniya.
Boss Mustapha: Abin da sabon SGF ya ce game
Lawal da Buhari
Mustapha yayi wannan jawabin ne a
ranar Laraba a lokacin da ya shiga
ofishin sa bayan an rantsar da shi a
matsayin sabon seketaren gwamnatin
Boss Mustapha ya yaba da kokarin da Habiba Lawal ta yi a tsawon lokacin da
aka bata rikon kwaryar ofishin SGF tun
lokacin da shugaban kasa ya dakatar da
tsohon SGF Babachir David Lawal bisa
zargin aikata laifin cin hanci da rashawa.
Ya kara da cewa “hakkin mu ne mu
tabbatar da gwamnatin nan ta samu
nasara, dan idan ta gaza, wannan zai
nuna ba mu yi aikin mu da kyau ba.

Labels: