Boko Haram ta kwace garin Magumeri na jihar Borno a


Hakkin mallakar hotoGETTY IMAGESImage captionWata majiya a rundunar sojin kasar ta tabbatar da harin amma ba ta yi karin haske ba
Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun karbe iko da garin Magumeri da ke arewa maso yammacin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, kamar yadda rahotanni suka ce.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ce mutanen garin Magumeri sun shaida masa ta wayar salula cewa sun arce zuwa wani daji da ke kusa da su.
Wata majiyar soji ta tabbatar da cewa an kai hari garin, amma ba ta yi bayani game da ko maharan sun kwace garin ba.
A farkon watan da mu ke ciki ne,aka kashe mutum shida tare da kone gidaje masu yawa a harin da aka kai garin .
Mayakan Boko Haram sun kara zafafa hare haren da suke kai wa tun bayan daukewar ruwan sama a watan Satumba.
Wannan shi ne hari na baya bayanan tun bayan harin kunar bakin wake da aka kai a wani masallaci a jihar Adamawa, inda mutum 50 suka hallaka.
Harin na cikin hare hare mafi ya muni da aka kai tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya hau kan mulki a shekarar 2015, inda ya yi alkawarin kawo karshen masu tada kayar baya

Labels: