Bindiga daɗi: Wani Dansanda ya harbi wani ɗan kasuwa, a kasuwar Singa dake Kano 

Wani Dansanda ya harba ma wani dan kasuwa alburushi a kasuwar Singa dake jihar Kano, sakamakon tirjiya da Yansandan suka fuskanta yayin gudanar da aiki a kasuwar, inji rahoton Daily Trust.

Wannan lamari ya faru ne a ranar Laraba 29 ga watan Nuwamba, a daidai lokacin da tawagar jami’an hukumar yaki da jabun magunguna da abinci, NAFDAC tare da Yansanda suka dira kasuwar da nufin kama duk wasu jabun kayayyaki.

Sai dai majiyar Hausansi ta ruwaito da isar ayarin jami’an NAFDAC da Yansandan, sai suka ci karo da wasu gungun yan kasuwa, wanda suka tare musu hanya da nufin hana su shiga cikin kasuwan don gudanar da aikinsu.

Yansanda

Hakan ya janyo tirka tirka, inda har yan kasuwan suka kona tayoyi a kan hanyar shiga Bello road, ganin haka ya sanya Yansanda harba barkonon tsohuwa, tare da alburusai a sama da nufin tarwatsa jama’an.

Wani shaidan gani da ido yace a a sakamakon harbe harbe, harsashi ya samu wani Malam Garba Abubakar, wanda a yanzu haka yake samun kulawa a asibitin Mohammed Abdullahi Wase.

Sai dai Kaakakin rundunar Yansandan jihar, DSP Magaji Musa Majia yace bashi da masaniya dangane da lamarin, “A yanzu haka ina garin Abuja, inda na halarci wani taro, don haka bani da masaniya dangane da lamarin.” Inji shi.

Amma fa shugaban hukumar NAFDAC, Bashir Muazu ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace jami’ansu sun shiga kasuwar ne da nufin kwace kayayyakin bogi, da wadanda basu da lambar NAFDAC.

Labels: