Bani da masaniyar inda Kanu yake - Buratai ya shaidawa KotuĀ 

din da ta gabata da cewa, ta yi watsi da takunkumin tursasa shi akan sai ya fito da shugaban masu fafutikar neman kafa yankin Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu.

Wata kungiyar lauyoyi dake wakiltar shugaban na IPOB, ta nemi kotu da ta tursasa Buratai akan sai ya fito da Kanu da rai ko kuma kishiyar hakan.

Lauyoyin wanda Mista Ifeanyi Ejiofor ya jagorancin kungiyar sun shaidawa wa kotu cewa, "kawo wa yanzu, ba su sanya Kanu a ido ba ko su ji daga gare shi tun daga ranar 14 ga watan Satumba da dakarun sojin kasan suka kaiwa gidan Kanu farmaki, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi da har hakan yayi sandiyar salwantar rayuka 28 tare da cafke mutane kuma suka yi awon gaban da su."

Dangane da wannan tuhuma da lauyoyin ke yi akan rundunar sojin kasan Najeriya da kuma tanadi da kundin tsarin mulkin kasa karkashin sashe na 12, ya sanya suke bukatar kotu ta umarci shugaban rundunar da ya bayyanar da Kanu a gaban kotu.

Shugaban hafsan Sojin kasa Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai

Sakamakon kalubalantar wannan hamayya ne, ya sanya Buratai ya gabatar da takardar shaida a gaban kotu, da take nuna cewar Kanu bai kasance a hannun rundunar sojin kasan ba.

"Sabanin tuhumar da lauyoyin ke yi a gaban kotu, sojin kasan da suka gudanar da atisayen Python Dance II a yankin Kudu Maso Gabashin kasar nan, ba su gadar da wata alaka da Kanu ba a ranar 12 ko 14 ga watan Satumba, da ma dukannin wata rana da ta biyo baya kamar yadda ake tuhumar."

"Takardar shaidar ta ci gaba da cewa, Kanu ba ya tare kuma bai taba kasancewa a hannun mutum guda ko wata kungiya da take bin umarnin Buratai kai tsaye ba."

"Babu ko sojin kasa guda da ya kama ko ya tsare Kanu a yayin da sojin ke yankin har kawo wa yanzu."

"Kuma tuhumar da ake yi na farmakin sojin kasan a yankunan Kudu Maso Gabashin kasar musamman gidan Kanu gaba daya zance ne na shaci fadi domin babu kamshin gaskiya ko da ta kwayar zarra."

Buratai ya shaidawa kotu cewa, "a yayin da sojin kasan ke gudanar da atisaye cikin lumana mai taken Python Dance II, sun bi wata motar daukar kaya a ranar 14 ga watan Satumba makire da muggan makamai har wani gida wanda bincike ya nuna cewa ai gidan da motar mallakin Kanu ne da mahaifin sa"

Hausansi ta ruwaito da sanadin jaridar Daily Post cewa, wannan motar daukar kaya da mutanen cikin ta sun kalubalanci umarnin sojin na tsayawa a bincike su, da har ya sanya sojin su ka bi wannan mota, sai dai ba harbi ko kuda ya faru domin tsare lafiyar al'umma.

Labels: