Babu Fulani makiyayan da ya fada cikin kogin Binuwai

- Gwamnatin jihar Binuwai ta muzanta rahoton cewa wani bafilatani ya fada a cikin kogin Binuwai

- Gwamnati ta ce wannan labari farfaganda ce kawai

- Babban sakataren gwamnati ya ce sun tuntube 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro, amma babu tabbacin hakan ya faru

Gwamnatin jihar Binuwai ta karyata rahoton da ta bayyana cewa wani bafilatani, Mohammed Abdulkadire, mai shekaru 56 da haihuwa ya fada a cikin kogin Binuwai wanda ke yankin karamar hukumar Logo na jihar, game da shanun sa da suka ɓace.

Gwamnati ta bayyana labarin a matsayin farfaganda.

Shugaban kungiyar Fulani makiyaya watau Miyietti Allah a jihar Binueai, Garus Gololo ya yi ikirarin cewa Abdulkadire ya kashe kansa bayan mutuwar shanun sa fiye da 200 sakamakon mumunar yunwa da kishin ruwa bayan kaddamar da dokar hana kiwo a jihar.

Gwamnan jihar Binuwai

Da yake mayar da martani akan lamarin, babban sakataren labarai ga gwamna Samuel Ortom, Tever Akase ya bukaci al’umma su yi watsi da labarin.

Idan dai baku manta ba Hausansi ta ruwaito cewa kungiyar Fulani makiyaya ta bayyana takaicin ta game da dokar haramtawa makiyaya yin kiwo a jihar, inda ta ce dokar ta jawo asarar shanu fiye da 600 saboda rashin abinci da ruwa.

Akase ya ce: “Mun tuntube 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro, amma babu tabbacin cewa wani bafilatani makiyaya ya fada cikin kogi a Logo ko wani ɓangare na jihar Binuwai”.

"Hakazalika, jami'an tsaro ba su da tabbacin cewa Fulani makiyaya sun rasa shanu 600 a jihar”.

Labels: