Babbar magana: Saudiyya ta bullo da hanyar samun kudi daga hannun Mahajjata

Kasar Saudi Arabiya za ta rika aiki da takardun biza daga badi

- A da can ba a bukatar biza wajen shiga aikin hajji da na umrah

- Yanzu dai Kasar na neman kudin bayan karayar tattalin kasa

A halin yanzu mun samu labari daga kafafen yada labaran Kasar waje cewa Kasar Saudi Arabia za ta fara yi wa masu zuwa ziyara takardar biza daga shekara mai zuwa.

Kasar Saudi za ta fara yi wa Mahajjata biza

Kasar Saudi Arabiya za ta kawo hanyar samun kudi daga bakin ta don kuwa ana kokarin kawo sauyin da zai sa a rika bukatar takardun biza daga bakin da ke zuwa aikin Hajji ko Umrah a Garuruwan na kasa mai tsarki da ke Saudi Arabiya.

Kamar yadda labari ya kai gare mu daga shekara mai zuwa ta 2018 kamar yadda wani babban Jami’in Kasar Yarima Sultan bin Salman ya bayyanawa gidan jaridar CNN za a bukaci biza. A da can ba a bukar biza domin shiga kasar yin aikin Hajji.

Kasar Saudiyya na san ran yawan mahajjata su karu daga sama da Miliyan 16 har zuwa akalla miliyan 30 daga bana zuwa shekarar 2030 inda za a rika kashe akalla Dala Biliyan 47 a kowace shekara. Hakan dai za kawowa Kasar kudin shiga.

Labels: