Gwamnatin tarayya ta jaddada alkawarinta ga yaki da rashawa ba tare da nuna banbanci ba
- Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa ya ce gwamnatin shugaba Buhari baza ta bar masu laifi ba tare da hukuntasu ba
- Adesina ya ce shugaban yana nan akan al’amarin Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar dake kula da harkokin fansho
Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, a ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba, ya ce shugaba Muhammadu Buhari yana kan alkawarinsa na yaki da rashawa ba tare da nuna banbanci ba.
Gidan talbijin din Channels ta rahoto cewa Adesina ya lura cewa yan Najeriya zasu samu labari daga shugaba Buhari kan al’amarin da ya shafi Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban hukumar fansho
A cewar shi: "Kamar yanda gwamnati take nuna damuwa, al’amari ne da za’a warware."
Ba’a yi watsi da al’amarin Maina akwandon shara ba – Fadar shugaban kasa
Maina, wanda aka yi wa zargin almubazaranci da kudin fansho kimanin naira biliyan 2, ya koma bakin aiki a matsayin ma’aikacin gwamnatin tarayya bayan hukumar EFCC ta bayyana tana neman shi.
Komawar bakin aikinsa ya janyo maganganu daga yan Najeriya, al’amari da wassu suke ikirarin cewa hakan ne ya sa shugaba Muhammadu Buhari ya bada umurni sauke shi da gaggawa.
A mayar da martani ga jiran cewa gwamnati zata bada umurnin binciken al’amarin, Adesina ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci rahoto kan sha’anin da ya kai ga komawar Maina aikin gwamnati.
Labels: Labarai