Ba sani, ba sabo: EFCC ta gurfanar da wani jigon jam’iyyar APC kan badaƙalar naira biliyan 3.2 

Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta zo da wani sabon salo da ba’a saba gani ba a siyasar Najeriya, ta yadd da zarar wani dan siyasa dake da kashi a gindinsa ya shiga jam’iyya mai ci, shikenan ana yafe masa.

An cigaba da shari’ar jigon jam’iyyar APC a yankin jihohin inyamurai, kuma tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu, wanda ake tuhumar kan karkatar da naira biliyan 3 da miliyan 200.

Shi dai wannan shari’a an fara shi ne tun a shekarar 2007, amma saboda kwan gaba kwan baya da ake samu, tare da dabarbarun lauyoyin wanda ake kara, hakan ya dinga kawo ma shari’ar tsaiko.

Orji Kalu

Mai shari’a Mohammed Idris na babban kotun tarayya na jihar Legas ne ya suararon karar, tun bayan da kotun koli ta baiwa hukumar yaki da rashawa, EFCC damar gurfanar da shi akan tuhumen tuhumen da take yi masa a shekarar 2016.

EFCC na zargin Kalu ya aikatawa satar ne a shekarun da yayi mulkin jihar Abia, a tsakanin 1999-2007, inda ake tuhumarsa tare da mutumin da yayi masa kwamishinan kudi, Ude Udeogo.

Daily Trust ta ruwaito Kalu da kansa ya halarci zaman sauraron karar, inda lauyan EFCC Rotimi Jacobs ya bayyana masa dukkanin tuhume tuhumen da suke yi masa, da kamfaninsa Slok Nig Ltd, da kuma kwamishinansa, da yace sun kai tuhume tuhume 34, dukkaninsu sun danganci cin hanci da rashawa.

Labels: