Auren Dole: Yarinyar da aka sace ta samu kubuta daga fadar Sarki

An yi zargin cewar tun bayan sace Hauwa, na tsawon kwana hudu, an boye ta ne a fadar sarkin Gashuwa, Alhaji Abubakar Suleiman, domin mayar da ita addinin musulunci.

An sace wata yarinya, Hauwa Dadi, 'ya ga tsohon sakataren kungiyar kiristoci ta kasa(CAN), tare da kokarin mayar da ita musulunci domin aurar da ita ga wani matashi da suke karatu tare a wata makarantar sakandire mai suna Brighter Academy dake garin Gashuwa.

Auren Dole: Yarinyar da aka sace ta samu kubuta daga fadar Sarki

Hauwa, mai shekara 13, ta samu 'yancin ta jiya Lahadi bayan matsin lamba daga wata kungiya mai rajin kare kai ta Stefanos Foundation biyo bayan shigar da korafi da dan uwa ga Hauwa, Jonathan Dadi, ya yi.

Kakakin rundunar'yan sanda a garin Gashuwa, Joseph Aloefuna, ya tabbatar da faruwar al'amarin. Joseph ya ce "DPO ne ya shiga maganar bayan an kawo mana korafin duk da kasancewar ya sanar da ni abinda yake faruwa".

Sannan yaci gaba da cewa " Wani yaro da yake son Hauwa ake zargi da sace ta amma bayan kama yaron bisa zargin da sace yarinyar sai ya bayyana cewar tana fadar sarki domin tana son musulunta".

Hukumar makarantar da yaran ke karatu ta bayyana cewar tun farko saida hukunta yaron saboda kokarin tursasawa yarinyar yin soyayya duk da kasancewar ta karamar yarinya dake aji hudu na sakandire.

Labels: