Masu fada a ji a harkan man fetur sun yi karo da junan su game da binciko mai a Arewa
- A 'yan kwanakin nan ne a ka tilastawa NNPC binciko man fetur a Arewacin Najeriya
- Masana sun ce aikin banza kawai a ke yi. NNPC kuwa za ta cigaba da binciken muddin Buhari ya bayar da umurni
Masu fada aji a harkan man fetur ba su gushe ba su na karo da junan su game da binciko man fetur a Arewa, musamman da a yanzun har an kashe miliyan 3 na dalar Amurka ba tare da an samu nasara ba.
Jaridar Guardian ta ruwaito cewan masu goyon bayan cigaba da binciken, basu damu da barnar kudin da a ke yi ba sakamakon nasarar hakon mai da a ka samu a makotan kasashe irin su Nijar da Chadi.
Su kuwa masana ilimin hako ma'adanai su na tunanin aikin banza a ke yi.
Hausansi ta tattaro bayanan masana a inda su ke cewa, kowace yanki na Najeriya da albarkatun da Allah ya yi mata, ba zai yiwu man fetur da albarkatun da ke Arewa su zauna tare a wuri daya ba.
A tattaunawar da Jaridar Guardian ta yi da masana, sun ce shuwagabannin Arewa, cikin su har da Shugaban Kasa Buhari, sun matsa kan binciken wanda hakan na illata tattalin arzikin kasan. Kusan shekaru 40 kenan da fara binciko man fetur a Arewa, a ra'ayin wadansu ana hakan ne kawai don azurta kalilan din mutane.
Shi kuwa Shugaban NNPC, Maikanti Baru, ya ce ba za su gushe su na wannan bincike ba matukar umurni ne daga Buhari. Ya kuma ce a bisa binciken da su ka yi, nan ba da jimawa ba za'a iya samo man fetur mai yawa a Anambra, Bida, Benue, Chad, Gongola, da Sokoto.