A yayin ziyarar aiki na kwanaki biyu da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a yankin kabilar Ibo, wanda ya fara a ranar Talata, ya gamu da karramawa irin na al’adar ibo.
A jihar Ebonyi, shugaban sarakunan jihar, Eze Charles tare da sarakunansa, sun nada shugaba Buhari sarautar ‘Enyioma 1 of Ebonyi’, a harshe Hausa, Babban Abokin Ebonyi.
Haka zalika, sarakan basu yi kasa a gwiwa ba, har sai da suka sake nada shi wani sarautar ta daban, mai taken ‘Ochioha Ndi Igbo’, shugaban al’ummar Ibo.
Naɗin
Hausansi ta samo wannan rahoto ne daga shafin shugaban kasa Muhammadu Buhari dake kafar sadarwar Facebook, inda aka daura hotunan shugaba, tare da Sarakunan yayin nadin sarautar.
Naɗin
Shuagaba Buhari ya kai wannan ziyara ne da nufin nuna ma yan kabilar Ibo ana tare, tare da basu tabbacin cin gajiyar wasu manyan ayyuka da gwamantinsa zata gudanar a yankin.
Ga bidiyon nadin sarautar nan daga shafin Buhari Sallau:
Labels: Labarai