
- Kungiyar yan taáddan Boko Haram na ci gaba da tayar da hankula a jihar Bono
- Yan ta’addan na huce haushin su akan mutane bayin Allah yayinda sojoji ke koransu daga mabuyarsu
- Kauyen Maikadiri a karamar hukumar Askira-Uba dake jihar Borno ne sabon waje da suka kai hari
Akalla mutane biyu aka kashe sannan da dama sun ji rauni yayinda yan Bindiga da ake ganin yan Boko Haram ne suka kai hari kauyen Maikadiri a karamar hukumar Askira-Uba dake jihar Borno a daren ranar Asabar, jaridar Premium Times ta rahoto.
A cewar wata majiya daga Askira-Uba, maharani sun kai hari ga mazauna kauyen dake bacci da misalin tsakar dare sannan suka fara harbe-harbe ba kakkautawa.
“Sun kashe akalla mutane biyu sannan sun sanya ma wasu gidaje wuta, ciki harda na Hakimin Maikadiri”, inji Abbas Gava, kakakin yan bangan Najeriya, jihar Borno.
An kashe mutane biyu, an kona gidaje da dama yayinda Boko Haram suka kai hari kauyen Borno
“Harin ya afku ne tsakanin karfe 12 dare da safiyar Lahadi: sun kona wani SUV mallakar hakimin garin, sannan kuma suka tafi da wasu motocinsa biyu.”
Har ila yau da yake tabbatar da al’amarin, wani mamban majalisar dokokin jihar Borno, Abdullahi Askira yace kauyen Maikadiri da kewayenta sun fuskanci hare-haren Boko Haram saboda suna da kusanci da iyakokin dajin Sambisa.
Dan majalisa yace Makadiri da Muthaku sun kasance kauyuka biyu a yanki daya da basu samu tsaron sojoji duk da kusancinsu da dajin Sambisa.