An daure wasu 'yan Najeriya a Ingila bisa damfarar kudi

- Sun hada baki su biyar sun damfari wani kamfani

- 'Yan sanda sun yi wuf sun yi amfani da fasha sun gano inda suke ta waya sun kame su

- An kwato kudin gaba daya

Wata kotun Ingila ta garkame wasu 'yan Najeriya su biyar a gidan yari saboda satar kudin wani kamfani har £610,000 daga asusun banki.

Jaridar Newham Recorder ta baiyana cewa Victor Oke, 39, mai zama a unguwar Barking a Landan, ya hada baki da Desmond Uyiosa Abifade, 25, dan unguwar Stratford, sun saci fuskokin darektocin kamfanin sun yi wa bankin su da suke ajiyar kudin waya sun kwashe kudin.

'Yan Najeriya da aka kulle a kurkuku a Ingila saboda damfara

Da suka damfari bankin sun aika da kudin zuwa wani asusun bogi na Moses Kuye, 28, dan unguwar Silvertown.

Sun yi amfani da Melinda Mensah-Oke, 37, matar Victor don ta yi muryar macen darektar kamfanin. Shi kuma Arinola Kuye, 27, dan-uwan Moses Kuye, ya yi musu safarar kudin.

An gano su ne da hukumar binciken damfarar bankin HSBC suka sha jinin jikinsu a kan wannan aiken kudin da suka yi; suka yi sauri suka daga maganar zuwa 'yan sandan binciken satar kudi don su gudanar da bincike.

Yan sandan sun yi amfani da fasaha sun gano daga ina suka buga wayar, wace irin waya ce, da kuma inda suke zaune.

Alkalin da ya saurari karar ya aika da Oke shekara hudu a gidan yari, Moses kuma an bashi shekara uku da wata uku. Mensah-Oke an bata wata goma sha hudu, Abifade kuma an bashi shekara biyu. Arinole Kuye kuma an bashi sharar titi har na shekara guda ba biya.

'Yan sandan sun samu sun kwato kudaden ba ko nairar da tayi ciwon kai.

Labels: