- PDP tace ta yi kuskure a baya amma ayi hakuri za a gyara
- Farfesa Jerry Gana ne yayi wannan kira ga ‘Yan Najeriya
- Gana yace al’umma sun gaji da APC sun kosa PDP su dawo
A cewar wani babba a Jam’iyyar PDP mai adawa Farfesa Jerry Ghana yace ‘Yan Najeriya sun gaji da mulkin APC kuma Jam’iyyar PDP kawai su ke jira ta dawo mulki Inji Jaridar Daily Trust.
Jerry Gana da wasu 'yan siyasar kasar
Jerry Gana yace APC ta ba Jama’a kunya don haka al’umma duk sun kosa PDP ta dawo mulki. Gana ya bayyana wannan ne wajen wani taron jam’iyyar tare da daya daga cikin masu neman Shugabancin PDP a Kasar Farfesa Tunde Adeniran.
Farfesa Gana yace ‘Yan kasar sun gaji da Jam’iyyar APC don haka kowa yake jiran Jam’iyyar ta su ta PDP ta shirya domin dawowa mulkin kasar a 2019. Tsohon Ministan yayi kira ga ‘Yan Jam’iyyar su zabi Shugaba na gari idan zabe ya zo.
Jerry Gana wanda yana cikin manyan Jam’iyyar ya bayyana cewa PDP ta san tayi kuskure kuma don haka ta ke ba ‘Yan Najeriya hakuri ta na kuma tabbatar da cewa za su gyara nan gaba. Jam’iyyar adawar dai ta dage sai ta karbi mulki a 2019.
Labels: Labarai