Yan fashi sun kashe jigon PDP, da wasu 4 a Zamfara

A ranar Juma’a wasu da ake zargin yan fashi ne sun kai hari sannan sun kashe wasu mutane biyar ciki harsa wani jigon PDP a jihar Zamfara, Alhaji Abdulhadi Saidu Garkuwan Yan ware. An kuma kawo cewa yan fashin sun rufe wani hanya a tsakanun Funtua zuwa Gusau inda suke ta harbin ababen hawa dake zuwa daga nesa. Sun tsayar sannan suka kashe mutanen dake cikin motan kafin su wargazar dasu da kayayyakin su. Wani mazaunin garin Alhaji Saidu Maishanu Gusau ya fada ma jaridar Daily Trust cewa an harbi jigon na PDP ne a wuya bayan motar su ta daki hanyar da mayakan suka toshe. Sun bude ma ayarin motocin jigon na PDP wuta. “Suna a hanyarsu ta dawowa daga jihar Kaduna inda sukayi wani ganawa basu san cewa yan bindigan na fashi a hanyar ba. Direban motan ya rayu amma dai yana karkashin kulawar likita a karamar hukumar Tsafe dake jihar,” inji shi.

Labels: