Tofa: Wani Dalibi ya maka Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya a Kotu

Wani Dalibin PhD a ABU ta Zariya ya maka

Jami’ar Kotu
- Jamilu Auwalu yana karar Malamin sa Dr.
Abubakar Yahaya
- Haka kuma Dalibin ya nemi Jami’ar ta biya
sa wasu kudi
Jaridar Daily Trust ta rahoto yadda wani
Bawan Allah mai karatun Di-gir-gir a
ABU ya kai wasu Malaman sa Kotu. Ba
dai yau aka saba kukan Jami'o'in na
matsawa Dalibai lamba ba.
Wani Dalibin Jami’ar Ahmadu Bello ta
Zariya ya maka Jami’ar kara a Babban
Kotun Tarayya da ke Garin Kaduna inda
ya nemi a biya sa kudi har Naira Miliyan
20 saboda bata masa lokaci da dukiya da
su kayi. Za a zauna ne dai a Kotu a
tsakiyar watan gobe.
KU KARANTA: An maka wani Dan Najeriya
kurkuku a Amurka
Jamilu Auwalu Adam wanda yake
karatun PhD watau Digiri na uku a fannin
lissafi ya bayyana yadda Dr. Abubakar
Yahaya wanda shi ne aka sa ya duba
kundin aikin sa ya matsa masa lamba
dalilin bai sa sunan sa a aikin sa da ya
buga a wata mujalla ba.
Haka kuma Dalibin yana karar Farfesa
Babangida Sani wanda yana cikin masu
duba aikin na sa. Wannan Bawan Allah
ya fara karatun ne a 2014 inda ya nemi a
hukunta Malamin na sa don ma bai kai
matsayin duba aikin mai Digiri na uku ba
kuma a nema masa wani Malamin.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar
ba mu labari, a tuntube mu a

Labels: