Shekarau na son tikitin 2019 a karkashin PDP
- Kwankwaso na son tikitin APC a zaben 2019
- Dukkaninsu daga Kano suke
A shirin 'yan siyasa da ake yamutsawa a jihar Kano, tsofin jiga-jigai a Jihar na ta sake lissafin yadda zasu kafa gwamnati a jihar, rigima da sun saba tun shekarun 2001, lokacin da aka karbi shari'ar musulunci a jihar ta Kano.

Siyasar Kano a 2019: Tsakanin Shekarau da Kwankwaso wa zai barma wani?
Sai dai, kama ma a iya cewa, dukkaninsu, masu neman dora gwamnonin, na yin haka ne ta hanyar neman babbar kujera a Tarayya, domin samun tagomashin masu yada labarai.
A PDP, malam Ibrahim Shekarau ya nuna aniyarsa ta takarar shhugabancin kasa, duk da ya gwada hakan a 2011 kuma bai kai labari ba.
Shima Kwankwaso, ya nuna aniyarsa ta tsayawa takara a APC a 2019, fastocinsa sun cika ko ina a kudu da arewar kasar nan, ko hakanna nufin zai iya ture mai mulki Buhari?
Sabon salo dai na iya juya siyasar Kano na nufin sai kayi rawa a can sama, sannan ne na kasa zasu bi, musamman idan kana watsa tsaba, kuma ga dukkan alamu, hannu daya ne a tafiyar ke da karfi ko siyasar watsa wa.
Shi dai Ganduje yana can gee ya dogara da shugaba Buhari, su kuma 'yan banga suna ta sare kan junansu da sunan siyasar zaamani.