Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, KSCB, ta musanta jita-jita dake yawo a gari cewar ta umarci kungiyar masu shirya fina-finai ta MOPPAN data mayar da Rahama Sadau bakin aiki.
Sannan ya kara da cewa " Zamu goyi bayan duk matakin da kungiyar MOPPAN ta dauka a kan Rahama Sadau, amma maganar gaskiya bamu umarci a dawo da ita ba, illa iyaka idan kungiyar da kanta tayi na'am da nadamar data yi kamar yadda ta aike mana gabadaya a rubuce, ta dawo da ita, mu bamu da haufi a kan hakan, saidai ba zamu yi wani yunkuri na ganin kungiyar ta janye matakin data dauka a kanta ba".
Kungiyar MOPPAN ta kori Rahama Sadau daga kamfanin shirya fina-finai na Kannywood ranar 3 ga watan Oktobar 2016 bayan data fito cikin faifan bidiyon wata waka da kungiyar tace ya sabawa dokokinsu na sana'ar wasan kwaikwayon Hausa.

Daraktan hukumar tace fina-finai ta Kano, Isma'il Na'abba Abdallah, ya bayyana hakan a wata ganawa da kamfanin jaridar Daily Trust ta waya. Jita-jitar mayar da Rahama Sadau din dai ba zata rasa alaka da wani hoto da Sadau din tayi da shugaban hukumar tace fina-finan tare da shahararren jarumin wasan Hausa, Ali Nuhu, Sannan da fitowar data yi kafafen yada labarai a jihar Kano ta bayar da hakuri ga Gwamnan jihar da kuma sarkin Kano bisa fitowar ta cikin wani faifan bidiyon waka da bai yiwa jama'ar Kano dadi ba. Ali Nuhu, Afakallah, da Rahama Sadau Afakallah ya bayyana cewar "Abinda ya faru shine, Ali Nuhu tare da darekta Yaseen Auwal sun rako Rahama Sadau ofishina, kuma bisa tattaunawar da mukayi na fahimci tayi nadamar abinda ta aikata kamar yadda kowa yaji da kunnensa a gidajen Rediyo".