El-Rufa'i ya mayar wa da kotu martani a kan cewa sai jihar Kaduna ta biya Audu Maikori kudi

Maikori ya kai jihar Kaduna kara a kotu a kan cin zarafin sa da aka yi - An kama shi ne a bisa zargin tada tarzoma a cikin al'umma ta yanar-gizo. - Kotu ta ce an ci zarafin sa, sai an biya shi miliyoyin kudi Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru el-Rufa'i ya ci alwashin daga karar hukuncin da babbar kotun kasa ta zartar a kan sai jihar ta biya Audu Maikori kudi har Naira miliyan 40 saboda cin zarafin sa da ya ce an yi. El-Rufa'i ya ce har kotin koli za su iya zuwa. Audu Maikori Maikori shine shugaban Chocolate City Entertanment. Ya shigar da kara kotu ne a ranan 5 ga watan Mayu a kan cewa gwamnati ta sa an kama shi a kan zargin ingiza jama'a. Ya kai karar gwamnatin Kaduna, kwamisionan 'yan sandan Kaduna, da shugaban lauyoyin jihar. An kama Maiori ne a bisa zargin ya hau kafar Tuwita yana yada maganganun da zasu jawo tashin hankali a cikin al'ummar Kaduna. Alkalin da ya saurari karar, John Tsoho, ya ce sai sun biya shi har Naira miliyan 40 saboda an bata masa suna, ya sha duka hannun 'yan sanda, sannan kuma da kudin da ya kashe don neman magani bayan an sake shi. Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada :

Labels: