Wani hoton da ya bulla a dandalin zumunta a satin da ya gabata na ci gaba da daukar hankulan jama'a da dama na Jarumar nan ta wasannin fina-finan Hausa Halima Atete da kuma tsohon Gwamnan Kano Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a filin jirgi. Hoton dai na kunshe ne da jarumar zaune a kusa da shahararren dan siyasar inda ta dora wata jar hula da ke nuna alamun mubayi'a ga bin tafarkin Kwankwasiyya karkashin jagorancin tsohon Gwamnan. Dandalin Kannywood: Jaruma Halima Atete ta gamu da masoyin ta Sanata Kwankwaso a Dubai
Hausansi dai ta samu daga majiyoyi da dama cewa an dauki hoton ne a filin sauka da tashin jirage na kasa-da-kasa dake a garin Dubai a dunkulalliyar Daular Larabawa. Da ma dai ba tun yauba jaruman dake shirya fina-finai a jihar ta Kano din suna nuna matukar kaunar su ga tsohon Gwamnan da suke kallon yana maraba da sana'ar ta su.
An haifi jariri da sunan Allah rubuce a kunnuwansa a jihar Gombe