2019: Manyan 'Yan wasan Kannywood su na goyon bayan Atiku

'Yan wasan kwaikwayo a Najeriya na
marawa Atiku baya
- Ana tunani Atiku zai tsaya takarar
Shugabanci a 2019

- Irin su Fati Muhammad su na tare da
babban Dan siyasar
Mun samu labari daga Abu Sidiqu cewa
wasu 'Yan wasan fim sun yi wani taro a
Garin Kaduna inda har su ka nuna
alamun marawa Alhaji Atiku Abubakar
baya a zabe mai zuwa.
'Yan wasan fim na Kannywood na
marawa Atiku baya bisa dukkan alamu.
Irin su Fati Muhammad su ka halarci
taron inda aka kara mata girma a harkar.
Sauran manyan Taurari irin su Adam
Zango da Rabiu Rikadawa da wasu
Darektoci ma ba a bar su a baya ba.
KU KARANTA: Rikicin neman kujerar
Shugabancin PDP
Sauran wadanda su ka halarci taron a
Kaduna sun hada da Abida Mohammed
da Fati Washa, Sadiya Gele, Tahir I. Tahir,
Shamsu Cash Money, Abbas Sadik, Mama
Binta, Binta Kofarsoro, Fati Yola, Fati
Mama, Hadiza Kabara, Fati K.K., da dai
sauran su.
Ana tunani Wazirin Adamawa Atiku
Abubakar zai tsaya takarar Shugabanci a
2019. Kuma da alamu a wajen taron da
aka karrama Fati Muhammad sun nuna
goyon bayan su ga tsohon Mataimakin
Shugaban kasar Alhaji Atiku Abubakar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar
ba mu labari, a tuntube mu a

Labels: